Matthew 17

Sākewar Kamanni

1Bayan kwana shida, sai Yesu ya ɗauki Bitrus, Yaƙub da Yohanna ɗanʼuwan Yaƙub, ya kai su kan wani dutse mai tsawo, su kaɗai. 2A can aka sāke kamanninsa a gabansu. Fuskarsa ta haskaka kamar rana, tufafinsa kuwa suka zama fari fat suna walƙiya. 3Nan take sai ga Musa da Eliya suka bayyana a gabansu, suna magana da Yesu.

4Sai Bitrus ya ce wa Yesu, “Ubangiji, ya yi kyau da muke nan. In kana so, sai in kafa bukkoki uku—ɗaya dominka, ɗaya domin Musa, ɗaya kuma domin Eliya.”

5Yayinda yake cikin magana, sai wani girgije mai haske ya rufe su, sai wata murya daga cikin girgijen ta ce, “Wannan Ɗana ne, wanda nake ƙauna; wanda kuma nake jin daɗinsa ƙwarai. Ku saurare shi!”

6Saʼad da almajiran suka ji haka, sai suka fāɗi ƙasa rubda ciki, a firgice. 7Amma Yesu ya zo ya taɓa su ya ce, “Ku tashi, kada ku ji tsoro.” 8Da suka ɗaga kai, ba su ga kowa ba sai Yesu kaɗai.

9Suna cikin gangarowa daga dutsen ke nan, sai Yesu ya umarce su cewa, “Kada ku faɗa wa kowa abin da kuka gani, sai bayan an ta da Ɗan Mutum daga matattu.”

10Almajiran suka tambaye shi suka ce, “To, me ya sa malaman dokoki suke cewa, dole sai Eliya ya fara zuwa?”

11Yesu ya amsa, ya ce, “Tabbatacce, Eliya zai zo, zai kuma gyara dukan abubuwa. 12Amma ina faɗa muku, Eliya ya riga ya zo, ba su kuwa gane shi ba, amma suka yi masa duk abin da suka ga dama. Haka ma Ɗan Mutum zai sha wahala a hannunsu.” 13Saʼan nan almajiran suka gane cewa yana musu zancen Yohanna Mai Baftisma ne.

Warkarwar Yaro Mai Aljani

14Da suka isa wajen taron, sai wani mutum ya zo ya durƙusa a gabansa. 15Ya ce, “Ubangiji, ka yi wa ɗana jinƙai. Yana da farfaɗiya yana kuma shan wahala ƙwarai. Ya sha fāɗuwa cikin wuta ko ruwa. 16Na kuma kawo shi wurin almajiranka, amma ba su iya warkar da shi ba.”

17Yesu ya amsa, ya ce, “Ya ku zamani marasa bangaskiya da kuma masu taurin kai, har yaushe zan kasance tare da ku? Har yaushe kuma zan yi haƙuri da ku? Kawo mini yaron a nan.” 18Yesu ya tsauta wa aljanin, ya kuwa rabu da yaron, nan take yaron ya warke.

19Saʼan nan almajiran suka zo wurin Yesu a ɓoye suka tambaye shi suka ce, “Me ya sa ba mu iya fitar da aljanin ba?”

20Ya amsa ya ce, “Saboda kuna da ƙarancin bangaskiya sosai. Gaskiya nake gaya muku, in kuna da bangaskiyar da take ƙanƙanuwa kamar ƙwayar mustad, za ku iya ce wa wannan dutse, ‘Matsa daga nan zuwa can,’ zai kuwa matsa. Babu abin da zai gagare ku.”
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da kai. 21 Amma irin wannan ba ya fita, sai da adduʼa da azumi.


21
This verse is empty in this translation.
22Da suka taru a Galili, sai ya ce musu, “Za a bashe Ɗan Mutum, a hannun mutane. 23Za su kashe shi, a rana ta uku kuma za a tashe shi.” Almajiran kuwa suka cika da baƙin ciki.

Harajin Haikali

24Bayan Yesu da almajiransa suka isa Kafarnahum, sai masu karɓan harajin rabin shekel suka zo wurin Bitrus suka ce, “Malaminku ba ya biyan harajin haikali ne
da Girik dirakmas biyu
?”

25Ya amsa ya ce “I, yana biya.”

Da Bitrus ya shiga gida, Yesu ne ya fara magana. Ya ce masa, “Me ka gani, Siman? Daga wurin wane ne sarakunan duniya suke karɓar kuɗin shiga da kuma haraji-daga wurin ʼyaʼyansu ne ko kuwa daga wurin waɗansu?”

26Bitrus ya amsa, ya ce, “Daga wurin waɗansu.”

Yesu ya ce masa, “Wato, an ɗauke wa ʼyaʼyan ke nan.”
27“Amma don kada mu ɓata musu rai, ka je tafki ka jefa ƙugiyarka. Ka ɗauki kifin da ka fara kama; ka buɗe bakinsa, za ka sami shekel guda. Ka kawo ka ba su, harajina da naka ke nan.”

Copyright information for HauSRK